IQNA

Dubban Masallata  Sun Gudanar Da Sallar Idi A Masallacin Al-Aqsa A Yau

17:21 - July 09, 2022
Lambar Labari: 3487523
Tehran (IQNA) Falasdinawa 150,000 ne suka gudanar da Sallar Idin Al-Adha a Masallacin Al-Aqsa, sannan a lokaci guda kuma Palasdinawa na Zirin Gaza sun gudanar da Sallar Idi a wannan yanki da gwamnatin yahudawa ta ke ci gaba da yi wa kawanya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Asabar 9 ga watan Yuli ne aka gudanar da sallar idin al-Adha a harabar masallacin Al-Aqsa tare da halartar masallata kusan dubu 150.

Al'ummar Palastinu maza da mata da manya da yara da tsoffi daga yankuna daban-daban da suka hada da yankunan da aka mamaye da lardunan Yamma da Kogin Jordan da Quds suka iso suna kabbara zuwa masallacin Al-Aqsa, tare da shiga harabar masallacin, duk da irin tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka kan hakan.

Wasu gungun al'ummar Palastinu da aka haramtawa shiga masallacin Al-Aqsa bisa dokokin zalunci na gwamnatin sahyoniyawa, sun gudanar da sallarsu da addu'o'i a kusa da masallacin.

Falasdinawa masu fafutuka sun raba kyaututtuka da kayan zaki a kofar shiga da kuma cikin harabar masallacin Al-Aqsa ga yaran da suka halarci Sallar Idi na yau tare da iyalansu.

Duk da cewa tun da sanyin safiyar yau ne jami’an ‘yan sandan gwamnatin mamaya ke jibge a kewayen tsohon yankin birnin Kudus da lunguna da sako-sako na birnin, har ma da kama wasu matasan Palastinawa a kofar shiga  masallacin Al-Aqsa, amam duk da haka dubban musulmi sun gudanar da sallar idia  masallacin mai alfarma.

4069536

 

 

captcha